Accessibility links

Ana Tafka Fada A Birnin Gao


Dakarun Mali a lokacin da suke zagaye a garin Gao. Fabrairu 20, 2013.

An yi musayar wuta tare da tada nakiyoyi a birnin Gao dake arewacin kasar Mali, inda dakarun kasar da na Faransa da kuma dakarun yammacin Afrika suke yakar mayakan kishin Islama.

Jami’an ma’aikatar tsaron kasar Mali sun bayyana yau alhamis cewa, an fara musayar wuta ne bayan harin da mayaka suka kai a Gao da tsakar dare, dakaru kuma suka shiga birnin domin kakkabe su. Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya laburta cewa, an cinnawa babbar kotun dake birnin Gao wuta.

Wani kakakin ministan tsaro ya shaidawa muryar Amurka cewa, an kwato birnin sai dai har yanzu ana fuskantar matsalar tsaro a wurin.

A halin da ake ciki kuma, shaidu da dakarun tsaro sun ce wani harin bom da aka kai kan wata mota a garin Kidal dake arewacin kasar ya jiwa a kalla mutane biyu rauni.

A wata sabuwa kuma, kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya buga rahoto cewa, an kashe a kalla mayaka 10 bayanda dakarun kasar Faransa suka bude wuta kan wata motar akori kura dake tafiya a arewacin Mali. Kamfanin dillancin labaran yace lamarin ya auku ne jiya Laraba yayinda rundunar ‘yan sanda ke farautar mayaka.
XS
SM
MD
LG