Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Bude Wuta A Wani Massallaci Dake Kenya


Mazauna wata unguwa a lokacin da suke duba wani waje inda fashewar bom ta auku.

‘Yan bindiga sun bude wuta a wani masallaci dake gabashin kasar Kenya, suka kashe a kalla mutane bakwai.

An kai harin ne yau alhamis a kauyen Maaleey, dake kusa da kan iyakar kasar Somaliya.

Jami’ai a kasar sun ce an kashe mutane biyar a cikin masallacin yayinda aka kashe wadansu mata biyu lokacin da suka yi kokarin shiga masallacin da gudu bayanda suka ji mutane suna ihu.

Kawo yanzu babu kungiyar da ta dauki alhakin kai harin.

Kenya tana fama da hare hare da suka hada da wadanda ake kaiwa da gurneti da ake dora alhakin kan mayakan al-Shabab na kasar Somaliya ko magoya bayansu.

Kungiyar al-Shabab taci alwashin ramuwar gayya bayanda dakarun kasar Kenya suka shiga kudancin Somaliya a watan Oktoba shekara ta dubu biyu da goma sha daya da nufin yakar kungiyar kishin Islaman.
XS
SM
MD
LG