Accessibility links

M23 Ta Cire Shugabanta Daga Mulki


'Yan tawayen M23 a lokacin da suke zaune a cikin wata mota garin Goma. Dec. 1, 2012 (file photo).
A cikin sanarwar da ta bada, kungiyar ta zargi Runiga da cewa ya bar wani tsohon babban kwamandan sojan Congo mai suna Bosco Ntaganda ya samu tasiri sosai a cikin kungiyar har ma ya janyo rigima a tsakanin su-ya-su ‘yantawayen.

Bertrand Bisimwa, kakakin kungiyar na fannin siyasa, ya gayawa sashen Faransanci na Muryar Amurka cewa tuni Runiga ya arce, watakila yaje ma ya hade da General Ntaganda.

A kalla mutane takwas aka kashe a kazamin fadan da ya barke ran Lahadin da ta gabata a tsakanin abinda wasu kafofi ce magoya bayan kwamandan mayakan kungiyar ta M23 ne Sultani Makenga da wasu dake goyon bayan wani madugunsu na daban.

Yanzu haka ma dai kungiyar ta M23 ta nada shi General Makenga a matsayin sabon shugabanta.
XS
SM
MD
LG