Accessibility links

Yarinya Mai Kwayoyin Cutar Kanjamau Ta Warke


Hoton wata yarin kennan da aka haifa da kwayoyin cutar kanjamau a garin Myanmar.

Likitoci anan Amurka sun ce wata ‘yar karamar yarinya da aka haifa da kwayoyin cuta dake haddasa kanjamu ko sida, ta warke bayan da aka cigaba da yi mata jinya akai-akai da mgaunguna da aka sani.

Yanzu ‘tana da shekara biyu da haifuwa daga jihar Mississipi dake kudancin Amurka, likitoci sunyi amfani da magungunan yaki da cutar sida daban daban uku, wadda suka fara bata sa’o’I 30 bayan an haifeta.

Likitoci suka ce ta warke’ ma’ana a gwajin da suka gudanar ba a ga kwayoyin cutar cikin jikinta ba, saboda haka babu bukatar a cigaba da yi mata jinya har na tsawon rayuwarta ba.

Wannan shine karo na farko da wani jaririya ko jariri da za a ce ya warke sumul daga wanan cuta.

Likitoci suka ce akwai bukatar a yi karin gwaje-gwaje domin gane ko irin wannan jinyar zata yi tasiri kan wasu yara da suke fama da wannan larura.
XS
SM
MD
LG