Accessibility links

Ministan Tsaron Faransa Ya Kai Ziyarar Bazata Zuwa Tsaunukan Mali


Shugaban Faransa a lokacin da yake ganawa da manyan hafsoshin soji.

Ministan tsaron Faransa ya kai wata ziyarar ba-zata a cikin tsaunukkan arewa-maso-gabashin Mali inda sojan faransa ke can suna yakar dakarun ‘yan kishin Islama.

WASHINGTON, D.C - Da sanyin safiyar yau Alhamis ne Jean-Yves Le drian ya iso garin Tessalit inda kuma ya gana da wasu daga cikin sojojin Faransa 4,000 da aka tura can Mali.
Ministan ya bayyana sojan na Faransa da cewa su “kamar wata gada ce da ake bi kanta…kuma su jarumawa ne dake cika aikin da Faransa ta aika su, suyi na jan daga da mayakan ‘yan ta’addar Mali.”

Shi wannan garin na Tessalit dai yana a cikin tsaunukkan Ifoghas ne inda sojan Faransa da na Mali ke farautan mayakan ‘yan kishin Islaman da aka koro daga arewancin Mali.
XS
SM
MD
LG