Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutan Kasar Venezuela Na Cigaba Da Jimamin Hugo Chavez


Shuwagabannin kasashen kudancin Amurka a bakin akwatin gawar shugaba Hugo Chavez.
Shuwagabannin kasashen kudancin Amurka a bakin akwatin gawar shugaba Hugo Chavez.

Al’ummar kasar Venezuela sun shiga rana ta biyu, ta ci gaba da juyayin rashin shugaban kasarsu Hugo Chavez, wanda ya rasu shekaranjiya Talata bayan ya jima yana fama da cutar kansa.

WASHINGTON, D.C - Yau ma dubban mutane sun cika makil a a wata makarantar horon soja dake birnin Caracas inda aka jiya gawar tsohon shugaban.

Yanzu haka manyan abokannin tsohon shugaban da suka hada da shugabannin kasashen Argentina, Bolivia da Uruguay suna can Venezuela don halartar jana’izar da za’a yi mishi gobe Jumu’a.

Kwamandan dakarun dake gadin gadar shugaban kasa Jose Omelia ya gaya cibiyar dillacin labaran AP cewa shugaba Chavez ya mutu ne bayan wani gagarumin fizgar zuciya da ya akama shi.

A can da gwamnatin venezulea ta gayawa duniya cewa Mr. Chavez yana fama da cutar sankara ne amma basu taba bayyana ainihin tsananin cutar ba.
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG