Accessibility links

Farmakin Duniyar Gizo Akan Koriya Ta Kudu Ya Zone Daga Chana


Wata na'ura da ta samu matsala kennan bayan harin duniyar gizo akan Koriya Ta Kudu.

Hukumomin Koriya ta Kudu sunce farmakin duniyar gizo da aka ai musu, wanda yassa komputocin tarin nakuna da kafofin watsa labarai bvarkatai suka ja suka tsaya, ya samo asali ne daga China.

WASHINGTON, D.C - Hukumar sadarwa ta Koriya ta Kudu tace wani binciken da aka gudanar ya nuna cewa adereshin komputar da aka yi anfani da ita wajen harbo annobar da ta tarwatsa na’urorin komputar wani banki na Koriya ta Kudu, ya fito ne daga China.

Sai dai kuma hukumar tace wannan ba wai lalle yana nufin daga China barnar ta samo sarsala ba, don ana iya cinna ta a wata kasar ta daban amma a nuna kamar ainihi daga China abin ya fito.

Akwai ma wani kakakin ma'aikatar harkokin wajen Koriya ta Kudu da ya fito balo-balo yana cewa kila shegantakar da makwapciyarsu Koriya ta Arewa ta fito tunda a can farko Koriya ta Arewa din ta taba cinna irin wannan ta’asar amma tayi anfani da adereshin China wajen aika barnar zuwa cikin Koriya ta Kudu.
XS
SM
MD
LG