Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Koriya ta Arewa Za Ta Bude Wani Rufaffen Masana'antar Nukiliya


Masana'antar Yongbyon a Koriya ta Arewa.
Masana'antar Yongbyon a Koriya ta Arewa.

Koriya ta Arewa tace zata farfado da ayyukan gidan makamashinta na Nukiliya mai sarrafa sinadarin Plutonium, kuma ta nuna alamun zata cigaba da tace sinadarin uranium. Wannan lamari dai ya kara zaman dar-dar da mutane suke fama da shi a wannan yanki.

Gidan talabijin din gwamnati, KCNA a takaice yau Talata yace yaji jami'ai suna cewa Koriya ta Arewa zata gyara, sannan zata cigaba da ayyuka a masana'arta ta Yongbyon domin hada makamai, da samar da makamashi da yayi kasar kadan.

Tace zata bude masana'anta domin sarrafa sinadarin uranium, da kuma injin da zai samar da megawatt 5 na wuta, wanda za'a iya amfani da karafunnan shi wajen samar da sinadarin plutonium din za'a iya hada makamai da shi. An rufe wannan waje a shekara ta 2007 bayan karbar tallafi da kasar tayi.

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon yau Talata yace kasar Koriya ta Arewa na kan hanyar karon battar karfe da sauran kasashen duniya, kuma wannan rigima na yanzu ya riga yayi tsawo. Yace yayi amanna babu wanda zai kai wa Koriya ta Arewa hari, yana mai cewa za'a tattauna domin warware matsalar.
XS
SM
MD
LG