Accessibility links

Jam'iyyar CPC Ta Jihar Borno Ta Shirya Hada Kai Da ANPP


Dan jam'iyyar CPC ne a nan ke rike da tutar jam'iyyar a lokacin gangamin yakin neman zaben shugaban kasa a Dandalin Mapo, dake birnin Ibadan.

Jam’iyyar adawa ta CPC ta jihar Borno ta shirya hada kai da jam’iyyar ANPP mai mulki domin kalubalantar jam’iyyar PDP dake mulkar Najeriya.

WASHINGTON, D.C - Jam’iyyar tace ta yanke shawarar yin haka bayan umarni da uwar jam’iyyar ta bayar da kuma nufin tallafawa jam’iyyar ANPP.

ANPP da APGA da CPC da kuma ACN sun soma tattaunawa watanni 3 zuwa 4 da suka wuce, domin su hada kai su kalubalanci PDP a zabuka masu zuwa.

Jam’iyyar CPC ta gudanar da taro a garin Maiduguri inda ta baiwa ‘ya’yan jam’iyyar damar tofa albarkacin bakinsu dangane da wannan

Wakilin Muryar Amurka, Haruna Dauda Biu ya hallarci wannan taro domin jin ta bakinsu.
Shugaban jam’iyyar CPC a jihar Borno Alhaji Ibrahim Al-Zubair ya kara da cewa zasu yi duk abinda ya kamata, domin kwato mulki daga hannun jam'iyyar PDP mai mulkar Najeriya.
XS
SM
MD
LG