Accessibility links

Ziyara A Bakin Daga A Borno Ta Janyo Ayar Tambaya

  • Garba Suleiman

FRundunar sojojin Najeriya ta ce ta karya lagon ayyukan Boko Haram a Maiduguri, amma har yanzu akwai dokar hana fita cikin dare a garin

Rundunar sojojin Najeriya ta zagaya da 'yan jarida cikin Maiduguri da kuma wasu sansanonin Boko Haram da ta fatattake su daga ciki

Rundunar sojan Najeriya ta bayyana daya daga cikin sansanonin 'yan Boko Haram da ta wargaza a zaman makeken sansanin horaswa wanda har akwai asibiti inda ta ke kula da 'ya'yanta da suka ji rauni, da kuma likita.

Mazauna garin Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, daya daga cikin jihohin da aka kafa dokar-ta-baci, sun ce sun yi imanin cewa lallai wannan wuri, inda aka ga konannun motoci da yawa, maboyar 'yan Boko Haram ne. Suka ce har yanzu 'yan Boko Haram su na kwace motocin mutane a cikin Maiduguri.

Wasu jami'an soja suka ce 'yan Boko Haram dake sansanin sun arce suka gudu a lokacin da sojoji suka iso. Aka ce wasunsu kuma, sun yi shiri da makamai masu yawa, an kuma gwabza da su.

Kakakin rundunar sojojin Najeriya, Birgediya-Janar Chris Olukolade, yace a saboda yawan dazuzzukan da suke arewacin Najeriya ba zai iya tabbatar da cewa babu wasu sansanonin na Boko Haram ba, amma kuma, abinda ya sa ke nan yanzu sun zuba idanu su na leka dukkan dazuzzukan dake yankin, in kuma sun gano zasu lalata.

Amma yace yana da kwarin guiwar cewa nan ba da jimawa ba, za a kawo karshen wannan artabu na 'yan Boko Haram da aka yi shekaru hudu ana fuskanta. Har ila yau ya musanta zargin cewa an kashe fararen hula, yana mai cewa duk wanda aka samu a cikin sansanin 'yan Boko Haram ba zai iya kiran kansa farar hula ba.

Har ila yau kuma, sojojin sun zaga da 'yan jarida wurare da dama inda 'yan Boko haram suka kai hare-hare.

Mutanen wani kauye mai suna Kirenowa, sun yi taro da sojojin, kuma sun fadawa 'yan jaridu cewa a can baya, 'yan Boko Haram su na kashe mutane, su kori wasu daga gidajensu tare da kwatar kudaden mutane.

Wani mutumin kauyen ya shaidawa 'yan jarida cewa a yanzu dai an samu kwanciyar hankali kadan a kauyen nasu, amma tun da aka fara aiki da dokar-ta-baci, ba su iya zuwa gonakinsu, kuma su na fama da karancin abinci sosai.

Har yanzu, gwamnati ba ta saki layukan wayoyi da na Intanet ba, a saboda haka yana da wuya 'yan jarida su san abubuwan da suke faruwa a bayan abubuwan da sojojin suka nuna musu.

Kungiyoyin kare hakkin bil Adama na kasashen duniya kamar Human Rights Watch, sun zargi sojojin Najeriya da laifin kashe daruruwan mutane tare da rufe wasu a kurkuku ba tare da an tuhume su da aikata wani laifi ba.

Wakiliyar Muryar Amurka, Heather Murdock, ta ce ba su jima da isa Maiduguri ba, aka tattara su aka maida su Abuja, kuma ba su samu zarafin kai ziyara domin ganin gidajen kurkuku, da asibitoci da kuma dakunan ajiye gawarwaki ba.
XS
SM
MD
LG