Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Bindiga Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Tsoffin Abokan Aikinsa Na Telebijin


Alison Parker tana hira da wata mata jim kadan kafin a bindigeta a kashe ta da mai dauka mata hoto yayin da jama'a ke kallo a telebijin.

An kawo karshen farautar Vester Flanagan, bayan da aka same shi cikin mota ya harbe kansa, a bayan da ya kashe wasu tsoffin abokan aikinsa na telebijin su biyu yayin da duniya ek kallo a telebijin

'Yan sanda a Jihar Virginia mai makwabtaka da Washington DC, sun kawo karshen frarautar dan bindigar da ya harbe ya kashe wasu 'yan jarida biyu yau da safe a jihar.

Dan bindigar da ake zargi, wanda tsohon dan jarida ne shi ma a gidan telebijin din da mutane biyun da ya kashe suke aiki, ya harbe kansa a lokacin da 'yan sanda suka tinkare shi a kan wata babbar hanyar motar dake bayan garin birnin Washington, DC.

Dan bindigar ya harbe ya kashe '[yan jaridar biyu a kusa da garin Roanoke a yankin kudu maso yammacin jihar Virginia.

'Yan sanda suka ce Vester Flanagan ya mutu a sanadin harbin kansa da yayi.

Dan bindigar ya bude wuta a kan 'yar jarida Alison Parker mai shekaru 24 da haihuwa, da mai dauka mata hoto Adam Ward dan shekaru 27 da haihuwa, a lookacin da suke hira ake nunawa kai tsaye ta telebijin a wani jerin shaguna dake Smith Mountain Lake kusa da garin Roanoke, kimanin kilomita 375 daga birnin Washington.

Da dan bindigar da kuma wadannan 'yan jarida biyu da ya kashe, duk sun yi aiki ma gidan telebijin na WDBJ-TV.

XS
SM
MD
LG