Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Thailand Ta Kama Wanda Take Tuhuma Da Hannu A Harin Bam


Adem Karadagdan kasar Turkiyya wanda 'yan sandan Thailand suka kama dangane da harin bam

‘Yan sanda a Thailand sun ce sun kama wani mutumi dangane da harin bam da ya kashe mutane akalla 20, ran 17 ga watan nan na Agusta a birnin Bangkok.

Masu magana da yawun ‘yan sanda sun ce yau asabar aka kama wannan mutumi a bayan garin birnin Bangkok, a bayan da ‘yan sanda suka gano wasu kayayyakin da watakila na harhada bam ne a wani gidan da yayi haya.

Wakilin VOA, Steve Herman, dake Bangkok, yace wani jami’in ‘yan sanda ya ce mutumin da aka kama wani dan kasar Turkiyya ne mai shekara 28 da haihuwa, mai suna Adem Karadag.

Babu wanda ya dauki alhakin kai hari kan wani wurin ibada mai farin jini da ake kira Erawan a tsakiyar birnin Bangkok. Hukumomi sun ce akwai ‘yan yawon shakatawa da bude ido da dama a cikin wadanda suka mutu. Wasu da dama sun ji rauni.

‘Yan sanda sun wallafa wani hoton da suka zana na wani mutumin da watakila dan kasar waje ne da ake kyautata zaton shi ya kai harin.

Hotunan bidiyon tsaro da aka wallafa sun nuna mutumin ya ajiye wata jakar da a farko take rataye a kafadarsa a kan wani benci dake wajen wurin ibadar na Hindu, ya tashi ya bar ta a wurin jim kadan kafin bam din ya tashi. Hukumomi sun yi imanin cewa yana da mataimaka amma sun bayyana tababa a kan ko yana da alaka da ‘yan ta’adda na kasa da kasa.

‘Yan sanda suka ce suna nazarin dalilai da dama da suka iya sanya kai harin, suna masu misali da kungiyoyin dake da hannu a rikice rikicen kasar, ciki har da Musulmi daga kudanci, ko ‘yan kabilar Uighur da suka fusata a bayan da Thailand ta mika ma kasar China wasu ‘yan kabilar su fiye da 100 a watan da ya shige.

XS
SM
MD
LG