Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Misra Ta Daure 'Yan Jaridar Al-Jazeera


Wakilan gidan telebijin na Al-Jazeera, Mohamed Fahmy,a tsakiya, da Baher Mohamed, a hagu, su na magana da 'yan jarida tare da lauyansu.

Alkali Hassan Farid yace wakilan uku na Aljazeera suna dauke da kayan aikin da hukumomin tsaron Misra ba su amince da su ba, kuma suna yin amfani da hotel dinsu a zaman cibiyar yada labarai ba tare da izni ba.

Wata kotun Misra ta samu wasu wakilai uku na gidan telebijin din Aljazeera da laifin goyon bayan kungiyar Ikhwanul Muslimun (Muslim Brotherhood) wadda aka haramta a kasar, ta kuma yanke musu hukumcin daurin shekaru uku uku a kurkuku.

Mai rikon mukamin darektan kamfanin Aljazeera, Mostefa Souag, ya bayyana wannan hukumci da aka yanke asabar a zaman na rashin kan gado wanda ya wuce tunani.

Nicholas Piachaud mai kula da harkokin Misra a kungiyar Amnesty International ya bayyana hukumcin da cewa misali ne na tauye ‘yancin fadin albarkacin baki kacokam da ke faruwa yau a kasar Misra. An daure ‘yan jaridar su uku ne kawai a saboda ra’ayoyinsu, in ji shi.

A lokacin da yake yanke wannan hukumci, alkali Hassan Farid yace wakilan uku na Aljazeera su na dauke da kayan aikin da hukumomin tsaron Misra ba su amince da su ba. Alkalin yace ‘yan jaridar su na yada labarum karya, sun kuma yi amfani da hotel dinsu a zaman cibiyar yada labarai ba tare da izni ba.

XS
SM
MD
LG