Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kalubalanci Gwamnatin Amurka Game Da Tafiyar Da Yakin Syria


Obama

Manyan jami’an diplomasiya 50 ne suka rattaba hannu wajen kalubalantar gwamnatin Amurka

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta tabbatar da sahihancin ikrarin da wasu kafofin diflomasiyyar cikin gida suka yi na cewa kusan manyan jami’an diplomasiya 50 suka rattabawa hannu wajen kalubalantar gwamnatin Barack Obama game da tafiyar da yakin Syria, da kuma amfani da hari ta sama akan gwamnatin kasar.

Wannan bayanai sun bayyana ne daga cikin kundin ‘yan adawa na cikin ma’aikatar harkokin wajen Amurkan, Kafar bayanan da ke bawa ma’aikata da jami’an diflomasiyya ma’aikatar damar bayyana ra’ayoyinsu.

Musamman ma’aikatan da basu yi na’am da yadda tsare-tsaren gwamnatin Amurka ke tafiya ba. Ta yadda suke bayyana kokensu a sirrance ba tare da fargabar gwamanti zata san su waye ba ko kuma yin ramuwar gayya.

Kakakin ma’aikatar wajen John Kirby ya tabbatar da sahihancin kundin bayanan amma bai yarda yayi magana akan abinda ya kunsa ba. Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya fadawa manema labarai a birnin Copenhagen cewa, bai ga kundin ba, amma zai duba idan ya dawo Washington

XS
SM
MD
LG