Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Zargi Amurka Da Karawa Ethiopia Karfin Guiwar Kaiwa Eritrea Hari


Eriteria ta fadawa kungiyar kare hakkin jama’a ta Majalisar Dinkin Duniya cewa kasar Ethiopia na shirin kaddamar da yaki gadan gadan akan yankin ta.

Gwamnatin kasar Eriteria ta fadawa kungiyar kare hakkin jama’a ta Majalisar Dinkin Duniya cewa kasar Ethiopia makwabciyar ta, tana shirin kaddamar da yaki gadan gadan akan yankin ta.

A kwanan nan sojojin Eriteria da Ethiopia suka yi arangama akan iyakar su.

Kasashen biyu suna zargin juna da laifin fara tsokanar fada, ciki harda mumunar gumurzun da suka yi a kewayen fagen dagan Tserona, wani yanki dake kudu da Asmara baban birnin kasar Eriteria.

A makon jiya ma’aikatar harkokin wajen Eriteria ta zargi Amirka da laifin cewa tana da hannu, wajen karawa Ethiopia karfin gwiwar harin da aka kai mata.

To amma mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amirka John Kirby yayi watsi da da zargin, ya mai

kira ga kasashen biyu da su yi aikin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

XS
SM
MD
LG