Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sake Bude Filin Jirgin Saman Istanbul


Filin Jirgin Saman Istanbul

Kamfanin jirgin saman kasar Turkiya yace ya koma ga dukkan zirga zirgan jiragen saman sa

An sake bude filin saukar jiragen sama na birnin Istanbul kasar Turkiya, bayan harin kunar bakin waken da aka kai jiya Talata da dare ya kashe mutane arba’in da daya da raunana fiye da mutane maitan.

Yau Laraba Prime Ministan Turkiya Binali Yildrrin ya bada wannan sanarwa.

Kamfanin jirgin saman kasar Turkiya yace ya koma ga dukkan zirga zirgan jiragen saman sa ciki harda na tsakanin birnin Istanbul da Amirka.

Gwamnan birnin Istanbul yace akalla mutane goma daga cikin wadanda aka kashe yan wasu kasashe ne, sa’anan kuma mutane dari da tara daga cikin mutane maitan da talatin da suka ji rauni an salamo su daga asibiti yau Laraba.

An bada rahoton cewa yan harin kunar bakin waken su uku sun harbi mutane da dama kafin suka tada bama bamai.

A wani labarin kuma, kasashen Rasha da Turkiya sun yarda zasu koma ga hadin kai akan harkokin bulaguro da harkokin kasuwanci tsakanin su. An cimma wannan daidaituwa bayan shugabanin kasashen biyu sun yi zantawarsu ta farko ta wayan tarho tun lokacinda kasar Turkiya ta kakkabo wani jirgin saman kasar Rasha a bara.

Haka kuma shugaba Vladimir putin na Rasha da takwaran aikinsa na Turkiya Recep Tayyip Erdowan sun amince zasu yi tazoli a watan Satunba a gefen taron kolin kungiyar kasashe masu arziki da ake cewa G 20 a takaice da za’a yi a kasar China.

XS
SM
MD
LG