Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Donald Trump Ya Kalubalanci Barak Obama Akan Satar Sauraron Wayarsa


Donald Trump

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya kalubalanci tsohon shugaban kasar Amurka Barack Obama, da Satar sauraron wayar Ofishinsa dake Trump Tower a Birnin New York kafin zaben shugaban kasa da akayi a watan Nuwambar shekara ta 2016.

A jerin rubutun twitter da yayi, Trump ya alakanta satar sauraron wayar da rikicin siyasa da aka tabayi a baya mai suna WaterGate a shekarar 1974 wanda yayi sanadiyyar saukar shugaban kasar Amurka na wannan lokacin Richard Nixon.

Trump dai bai bada wasu muhimman shaidu na yiwuwar Satar sauraron wayar ba.

A wani rubutun twitter da mai fashin baki kan harkokin tsaron na kasa da kuma bin kwakkwafin jami’an tsaro Officer John Schindler yace ta iya yiwuwa zargin da shugaban kasar yake yi ya shafi dokar bincikene kan jami’an tsaro na kasashen waje ta shekarar 1978 wacce ake kira FISA a takaice, wacce ta bada damar nadar bayanai tsakanin jami’an gwamnati da kasashen su na waje.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG