Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutteres Yayi kira Da A Dauki Matakin Gaggawa Akan Rikicin Myanmar


A karo na farko an yi maganar rikicin dake faruwa a Myanmar a bayyane a zaman da kwamitin sulhu da da tsaro na MajalisarDinkin Duniya.

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres jiya Alhamis, yayi kira da a dauki matakin gaggawa na hana mummunan yanayin da Jihar Rakhine dake Arewacin Myanmar take ciki, inda fiye da rabin Miliyan akasari Musulmai 'Yan kabilar Rohingya sun gudu zuwa makociyarta Bangladesh a watan da ya gabata.

Gutteres ya fada a wani zaman kwamitin sulhu da tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, yace “Al’amarin yana zama matsalar gaggawa ta yan gudun hijira fiye da ko wacce a fadin duniya.

Hukumar dai ta tattauna akan mtsalar sau uku a cikin sirri, a watan da ya gabata, amma wannan shine karo na farko tun a shekara 2009, da kwamitin yayi magana kan Myanmar a bayyane.

Gutteres yayi kira da akawo karshen shirye shiryen sojoji, wanda ya hana kayan agaji isa da kuma yan agajin gami da komawar yan gudun hijira zuwa wuraren su na asali cikin kwanciyar hankali.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG