Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ministocin Shugaba Buhari Sun Fara Gabatar Da Rahotanni Akan Ayyukansu


Shugaba Muhammad Buharii

Bisa ga umurnin da Shugaba Muhammad Buhari ya ba ministocinsa, sun fara gabatar da rahotanni akan ayyukansu suna bayyana nasarorin da suka samu da kuma kalubalen da suka fuskanta

Ministocin Shugaba Muhammad Buhari sun fara gabatar da rahotannin ayyukansu akan nasarorin da suka samu da kalubalen da suka fuskanta bisa ga umurnin shugaban.

Ministan wasanni da ci gaban matasa Solomon Dalung yana cikin ministocin da suka fara bayani akan nasarorinsu da kalubale kamar yadda ya yiwa manema labaru karin bayani bayan taron majalisar zartaswa na mako mako a Abuja.

A cewar Solomon Dalung ma'aikatarsa ta samu gagarumin nasara tun daga lokacin da gwamnatinsu ta hau mulki. Garambawul da suka yi ya basu nasararorin. Misali, minista ya daina nada shugabannin kungiyoyin wasa. Su ne zasu yi zabe su fitar da shugabanninsu.

Inji ministan Najeriya ta samu lambobin yabo da yawa a lokacinsu duk da cewa wasan baya bayan nan kungiyar kwallon kafar kasar ta sha kaye. Amma kasar za ta wasan kwallon kafar duniya da za'a yi a Rasha.

Ministocin ilimi da sufuri sun gabatar da nasu rahotannin. A fannin ilimi za'a gina bangaren koyas da shari'a a Jami'ar dake jihar Akwa Ibom. Haka kuma za'a gina wurin koyas da masu kashe gobara irin ta jirgin sama a makarantar horas da masu tukin jirgin sama dake Zaria.

Ga rahoton Umar Faruk Musa da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:29 0:00

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG