Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Muryar Amurka Tayi Fice a Bikin Talibijan da Finafinai Na Duniya


Muryar Amurka ta ci lambobin yabo

Muryar Amurka ta samu karramawa a bikin TV da Finafinai na Kasa da Kasa da aka yi a Las Vegas ranar 10 ga wannan watan.

Bikin da aka yi ranar 10 ga wannan watan na shekarar 2018, mai suna New York International TV and Film Awards, an yi ne a Birnin Las Vegas dake nan Amurka.

Muryar Amurka ta samu kyautar Zinari a fannin fina-fina da kyautar tagulla a wani fannin.

Shugabar Muryar Amurka Amanda Bennett ta ce “Ina alfahari da suka ciwo mana lambobin yabo. Nasarorin da suka samu sun nuna irin ‘yan jarida masu hazaka da muke dasu wadanda suke aiki dare da rana suke sadakar da rayukansu komi tsanani su kawowa masu saurarenmu sabbin abubuwa dake cike da Gaskiya da kuma kayatarwa”

Fim din nan akan Boko Haram mai suna “Tattaki Daga Bakar Akida” wanda ya bayyana ayyukan ‘yan ta’addan Boko Haram da suke yi da sunan addinin musulunci shi ya samu lambar yabo ta daya, wato lambar Zinari. Sai kuma shirin Off The Highway da ya zo na uku, wato ya samu tagulla

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG