Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Daruruwan Mutane Sun Yi Zanga-Zanga A Nijar


Daruruwan mutane sun yi maci yau alhamis a Yamai, babban birnin Jamhuriyar Nijar, suna neman da a sako wasu 'yan rajin haramta bauta su biyu da aka daure a kurkuku bisa zargin damfara.

'Yan sandan kwantar da tarzoma sun sanya idanu sosai kan wannan gangami, kuma babu wani rahoto na tashin hankali da aka samu.

Makonni da dama da suka shige, an kama wasu jami'ai biyu na kungiyar hana bauta mai suna Timidria, Ilguilas Weila da Alassane Biga, bisa zargin aikata damfara. Wannan zargi ya samo asali daga wani gangamin da aka shirya a cikin watan Maris inda a lokacin kungiyar ta ce za a saki bayi su dubu bakwai. Wadanda suka shirya gangamin suka ce jami'ai suka yi barazana ga wadannan bayi suka hana su zuwa wurin bukin.

Hukumomin Nijar sun tuhumi wadanda suka shirya gangamin da laifin neman kudi daga masu bayar da agaji ta hanyar haramuhn domin gudanar da wannan buki. Gwamnati ta ce an haramta bauta a kasar Nijar, kuma a yanzu haka babu wani bawa a kasar.

Amma kuma kungiyoyin yaki da bauta sun ce har yanzu mutum yana iya gadon bayin da suka yi aiki wa iyayensa. Suka ce akwai mutane fiye da dubu 40 dake aikin bauta a kasashen dake kewaye da hamadar Sahara, ciki har da jamhuriyar Nijar.

XS
SM
MD
LG