Al'ummar kasar Chadi suna jefa kuri'ar raba-gardama a kan ko zasu kawar da yawan wa'adin da shugaban kasa zai yi kan mulki a wannan kasa dake yankin tsakiyar Afirka.
An bhude rumfunan zabe tun da karfe 7 nna safe agogon kasar, kuma za a bar su a bude har zuwa karfe 6 na maraicen yau.
Hukumar zabe ta kasar Chadi ta ce mutane fiye da miliyan biyar suka yi rajistar jefa kuri'a, amma shugabannin hamayya sun ce magudi kawai aka yi wajen shirya kundin rajistar.
Amincewa da wannan sauyi ga tsarin mulki, zata bai wa shugaba Idris Deby damar neman wa'adi na uku kan karagar mulki a zaben da za a yi a shekara mai zuwa. 'Yan hamayya sun yi kiran da a kauracewa zaben raba-gardamar, suna fadin cewa wannan shiri yana mayar da kasar Chadi ta koma tamkar masarautar mutum guda.
A bayan sauyi ga tysarin yawan wa'adin da shugaba zai yi kan mulki, masu jefa kuri'a zasu kuma yanke shawarar ko za a rushe babbar majalisar dokoki ta kasa, watau majalisar dattijai.
Ana sa ran amincewa da wannan matakin.
Shugaba Idris Deby dai tsohon madugun 'yan tawaye ne wanda ya kwace mulki a wani juyin mulki a shekarar 1990.