Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Hezbollah Da Amal Sun Samu Gagarumar Nasara A Zaben Lebanon


Kungiyoyin Hizbullah da Amal masu gaba da bani Isra'ila, da kuma goyon bayan kasar Sham ko Syria a Lebanon, sun samu gagarumar nasara a zagaye na biyu na zaben 'yan majalisar dokoki da ake yi daki-daki a kasar.

Ministan harkoklin cikin gidan Lebanon, Hassan al-Sabaa, shi ya bayyana sakamakon zaben yau litinin. Ya ce kungiyoyin gwagwarmayar guda biyu sun lashe dukkan kujeru 17 na majalisar dokoki da aka yi takararsu, suka kuma lashe dukkan kujeru 6 da suka rage ba tare da hamayya ba.

A makon jiya, wata gamayyar masu adawa da kasar Sham dake karkashin jagorancin Saad Hariri, dan tsohon firayim minista Rafik Hariri, ta lashe zaben da aka yi a Beirut inda 'yan mazhabin Sunni suka fi yawa.

Wannan zabe da ake gudanarwa daki-daki har hudu, wanda za a kare a ranar 19 ga watan nan na Yuni, yana zuwa ne watanni hudu a bayan da aka kashe Hariri, abinda ya janyo zanga-zangar da ta tilastawa gwamnatin Lebanon ta sauka, ita kuma Sham ta janye sojojinta daga Lebanon.

Tun daga lokacin, Amurka da Majalisar Dinkin Duniya sun sake nanata kira ga 'yan Hezbollah masu gaba da Isra'ila da su ajiye makamansu. Kungiyar Hezbollah ta ce ko a mafarki ba ta da niyyar yin haka.

XS
SM
MD
LG