Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush yayi Jawabi Game Da Afirka


Shugaba Bush na amurka ya bayyana irin matakan da Amurka ke dauka na tallafawa Afrika, bayan da ya ki yarda da shirin Birtaniya na samar da karin agajin dala miliyan dubu ashirin da biyar kowacce shekara ga kasashen Afrika. Ga cikakken jawabin shugaban na Amurka:

Amerika tayi aiki tare da shugabannin Afrika wajen kirkiro da sabbin matakai masu nagarta na gabatar da sauye- sauye a nahiyar. Burinmu shine inganta rayuwar al’ummar afrika, kuma mun fara ganin sakamako. Taltalin arzikin kasashen afrika da dama yana bunkasa. A kasashen dake yankin kudu da hamada an samu bunkasar tattalin arziki fiye da yadda aka gani a shekaru takwas da suka shige. An sami wannan bunkasar tattalin arziki ne a saboda karfafa huldar cinikayya tsakanin nahiyoyin biyu. Bara na sa hannu a kan dokar bunkasa hulda tattalin arziki da kasashen afrika, wadda ta kawar da shingayen cinikayya, ta kara yawan kayayyakin afrika da ke zuwa nan amurka ta kuma samar da aikin yi ga yan kasar Afrika da amurkawa baki daya. Wannan yarjejeniyar tana karfafawa amurkawa guiwa su zuba jari a afrika tare da karfafa afrika suyi sauye sauye a harkokin kasuwancinsu.

Shugaba Bush ya kuma bayyana yawan tallafin da Amurka ta badawa a nahiyar Afrika shekarun da suka gabata: A bara yawan kayayyakin da Amurka ke aikawa a kudu da hamadar Sahara ya karu da kashi ashirin da biyar bisa dari. Yawan kayayyakin da Amurka ke shigowa da su daga wadannan kuma ya karu da kashi tamanin da takwas bisa dari. Wadannan nasasori da aka samu sun nuna cewa, jama’a a Afrika da kuma amurka suna kara yarda da cewa bude kasuwanni da kuma cinikayya sune hanyoyi mafiya sauri da nagarta na samun ci gaba a afrika. Kasashen dake cikin wannan yarjejeniya da amurka ta kulla na inganta tattalin arziki suna karfafa yin mulki bisa doka da kawar da shingayen cinikayya. suna kawar da danniya da cin hanci da kare ma’aikatansu tare da hana yara kanana yin ayyuka tamkar na bauta. suna zamowa abin koyi ga sauran kasashen nahiyar afrika. Kuma sun nuna cewa gwamnatocin da suke mutumta yancin al’ummarsu sun fi nuna kuzari wajen samun bunkasar tatalin arziki da kwanciyar hankalin siyasa. a yayin da muke karfafa cinikayya muna kuma sauya hanyoyin da muke bada agaji, mun yi shekaru da dama muna tura taimako a afrika ba tare da la’akari da yadda ake amfani da shiba. a karkashin gwamnatina an kara yawan agajin da ake ba kasashen afrika. amma ba wai karin agajin kawai muka yi ba, muna kuma bin sawu tare da la’akari da yadda ake amfani da wannan agaji. An fi yin amfani da kudaden agaji a kasashen da suke adalci a mulki, da mutunta doka da kyautatawa al’umma da kuma kula da tattalin arziki. Idan kasashe suka yi haka suka kuma samar da dama ga dukan al’ummara su, za a iya ciro kasa baki daya daga kangin talauci. a shekara ta dubu biyu da biyu mun kaddamar da asusun agaji da ake kira milleneum Challenge account domin samar da agaji ga kasashen afrika da suka fi fama da talauci bisa irin akidojin da na bayyana a sama. a cikin watan afrilu madagaska ta zama kasar farko da ta sanya hannu a kan yarjejeniya ta cin moriyar wannan asusu, kuma ina da karfin guiwa cewa sauran kasashen afrika zasu bi sawunta. a yayinda iskar walwala take kadawa a fuskar duniya, yana da muhimmanci nahiyar afrika ta zamo cibiyar damokaradiya da karuwar arziki da fata ta gari, inda mutane zasu iya rayuwa cikin koshin lafiya su kuma kasance suna da damar cimma burorin da suka sanya gabansu.

Afrika nahiya ce mai albarka, kuma Amurka tana so ta taimakawa nahiyar Afrika wajen cimma makoma maikyau da suka cancanci samu.

XS
SM
MD
LG