Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijeriya Za ta Kara da Morocco - Brazil Kuma Zata Gwabza da Argentina


Kasashen Afirka guda biyu zasu kece raini a gefe guda, yayin da a daya gefen kuma kasashen Amurka ta Kudu guda biyu su ma zasu yi kare-jini-biri-jini, duka a wurin gasar cin kofin kwallon kafar matasan duniya a kasar Netherlands.

A gwabzawar farko talatar nan, Brazil zata kara da babbar abokiyar tsamarta a fagen tamaula, Argentina a birnin Ultrecht. Kowace daya daga cikinsu ta taba lashe wannan kofi har sau hudu, abinda babu wata kasa ta duniya da ta taba yi. Brazil dai ita ce ke rike da kofin a yanzu haka, yayin da Argentina ce ta lashe uku daga cikin kofuna biyar da suka shige a wannan aji na 'yan kasa da shekaru 20.

'Yan Flying Eagles na Nijeriya suna murnar jefa kwallo
A wasa na biyu kuma, 'yan Flying eagles na Nijeriya ne zasu gwabza da 'yan Morocco. Babu wata kasar Afirka da ta taba lashe wannan kofi, amma Nijeriya ta je har wasa na karshe, amma ta fadi. Ghana ta taba zuwa wasan karshe har sau biyu ita ma tana faduwa.

Sai dai kuma, Nijeriya ta yi abin tarihi shekaru 9 da suka shige a lokacin da ta zamo kasar Afirka ta farko da ta taba lashe lambar zinare a wasan kwallon kafa na Olympics da aka yi a Atlanta a 1996.

XS
SM
MD
LG