Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sace Jakadan Misra A Kasar Iraqi


An sace jakadan kasar Misra a Bagadaza, ’yan makonni kalilan a bayan isarsa kasar Iraqi mai fama da yaki.

Jami’an jakadanci na Misra sun ce an sace jakada Ihab al-Sherif cikin daren jiya asabar daga babban birnin na Iraqi. Ba a bayar da karin hasken wannan al’amari ba, amma kuma kamfanin dillancin labaran Reuters ya ambaci wani jami’in jakadancin Misra yana fadin cewa malam al-Sherrif ya tsaya domin sayen jarida sai wasu motoci biyu cike da ’yan bindiga suka tsaya suka damke shi, suka yi awon gaba da shi.

’Yan sandan Iraqi sun killace ofishin jakadancin misra a yau lahadi domin kare ma’aikatan jakadancin kasar, wadanda yawancinsu an ce sun girgiza ainun da sace jakadan nasu da aka yi.

Jakada al-Sherrif ya isa Bagadaza a farkon watan jiya na Yuni, jim kadan kafin Misra ta bayyana maido da cikakkiyar huldar jakadanci da Iraqi. Misra ce kasar larabawa ta farko da ta yi haka tun bayan da aka hambarar da Saddam Hussein.

Sace jakadan na Misra yayi kama da sace wani babban jami’in jakadancin na Misra Mohammed Mamdouh Helmi Qutb, da aka yi a Iraqi. An saki wancan jami’in kwanaki uku bayan kama shi a bayan da Misra ta ce ba ta da niyyar tura sojojinta domin shiga cikin rundunar taron dangin da Amurka take jagoranci.

XS
SM
MD
LG