Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush yace Amurka Ta Bayar Da Muhimmanci Ga Batun Kawo Karshen Annobar Kanjamau A Afirka


Shugaba Bush ya ce Amurka ta sanya batun kawo karshen annobar cutar kanjamau a nahiyar Afirka ya zamo mai muhimmanci.

A cikin tattaunawar da yayi da Muryar Amurka, Mr. Bush ya ce shirin yaki da cutar kanjamau na gaggawa na dala miliyan dubu 15 da ya bullo da shi fiye da shekaru biyu da suka shige, ya doshi cimma gurinsa na taimakawa mutane miliyan biyu a Afirka wajen samun magunguna kashe kaifin cutar kanjamau nan da shekara ta 2008. Ya ce tuni ma shirin ya samar da magungunan yaki da kwayar halittar cuta ta HIV mai haddasa kanjamau ga 'yan Afirka dubu 230 a kasashen dake kudu da hamadar Sahara.

Amma kuma masu sukar lamirin gwamnatin shugaba Bush sun ce shugaban yana jan kafa wajen neman kudin gudanar da shirin nasa daga majalisar dokoki. Sun bukaci shugaba bush da ya samar da cikakken kudin gudanar da shirin nasa wanda ya fara bayyanawa duniya a jawabinsa na halin da kasa ke ciki a watan Janairun 2003.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa mutane miliyan 40 a fadin duniya suna dauke da kwayar halittar cutar HIV, kuma miliyan 25 daga cikinsu suna kasashen bakar fata na Afirka ne.

XS
SM
MD
LG