Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Fiye Da Miliyan Shida Suke Dauke Da Kwayar Cutar HIV Mai Haddasa Kanjamau A Afirka Ta Kudu - in ji Gwamnati


Wani sabon rahoto da gwamnatin Afirka ta Kudu ta bayar ya nuna cewa mutane fiye da miliyan shida ne suke dauke da kwayar halittar cutar nan ta HIV mai haddasa kanjamau a kasar. Wannan adadi kuwa ya zarce yadda aka yi tsammani tun da farko.

Ma'aikatar kiwon lafiya ta ce nazarin mata masu juna da aka yi lokacin awu a asibitoci cikin shekarar 2004, ya nuna cewa kimanin 'yan Afirka ta Kudu su miliyan shida da rabi ne suke dauke da wannan kwayar halittar cuta mai janyo kanjamau, ko SIDA.

Wannan adadi kuwa ya sha bam-bam sosai da wani nazarin da Hukumar Kididdiga ta kasar ta gudanar a farkon wannan shekara, wanda yayi kiyasin cewa mutane kimanin miliyan hudu da rabi suke dauke ad kwayar cutar a Afirka ta Kudu.

Jaridar "Business Day" ta ambaci babbar jami'ar da take kula da sashen bincike a ma'aikatar kiwon lafiya, tana fadin cewa an samu bambancin adadin ne a saboda bambancin matakan nazarin da aka yi amfani da su. Ta ce ma'aikatar lafiya tana yin amfani da matakan nazarin da Majalisar Dinkin Duniya ta tsara.

XS
SM
MD
LG