Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Akalla Tamanin Da Takwas Suka Mutu Ya Zuwa Yanzu A Hare-Haren Bam A Kasar Misra


Shugaba Hosni Mubarak na Misra ya ce hare-haren bam da suka kashe mutane akalla tamanin da takwas a cikin daren da ya shige a garin shakatawa na Sharm el-Sheikh mai farin jini a bakin gabar tekun maliya, sun kara karfi ne kawsai ga kudurinsa na yaka, tare da murkushe ta’addanci.

Wannan furuci nasa ya biyo bayan tashin bama-bamai akalla guda uku kusan lokaci guda a zauren tarbar baki na wani otel mai suna Ghazala Gardens, da wani wurin ajiye ababen hawa, da kuma wata kasuwa, jim kadan a bayan karfe 1 na daren da ya shige agogon kasar.

An yi imani da cewa akalla biyu daga cikin bama-baman an dana su ne a cikin mota.

Jami’ai sun ce akasarin mutanen da suka mutu ’yan kasar ta Misra ne, amma kuma an tabbatar da cewa akwai ’yan kasashen waje su takwas a cikin wadanda suka mutu. Mutane fiye da 100 sun ji rauni, da yawa daga cikinsu mai tsanani.

Ministan harkokin cikin gida na Misra, Habib al-Adli, ya ce akwai wani bayanin da aka samu mai nuna cewar akwai alaka a tsakanin wadannan hare-hare da wasu na bam da aka kai cikin watan Oktobar bara a kan garin shakatawa na Taba dake yankin Sinina, inda aka kashe mutane 34.

Har yanzu ba a tabbatar da gaskiyar ikirarin da wata kungiya mai suna Birged din Abdullah Azzam ta ’yan al-Qa’ida a Misra ta yi cewar ita ce ta kai wadannan hare-hare ba.

XS
SM
MD
LG