Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sarki Fahd Na Sa'udiyya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya


Sarki Fahd bin Abdul-Aziz na Sa'udiyya ya riga mu gidan agskiya.

Marigayi sarki Fahd, wanda aka fi karfafa zaton cewa shekarunsa an haihuwa 82 ne, ya jima yana fama da laulayi tun bayan ciwon kullutun jini mai haddasa shanyewar jiki da ya same shi a shekarar 1995. Nan da nan hukumomi suka bayar da sanarwar cewa dan'uwansa, Yarima Abdullahi mai jiran gado, wanda tun da Marigayi Sarki fahd ya fara rashin lafiya yake gudanar da harkokin mulkin wannan kasar da ta fi kowacce arzikin man fetur a duniya, ya gaje shi, ya zamo sarki.

Sarki Fahd bin Abdul-Aziz ya hau kan gadon sarautar Sa'udiyya a shekarar 1982, shekaru hamsin a bayan da mahaifinsa da ya shahara, Sarki Abdul-Aziz al-Sa'ud, ya hada kabilun yankin Arabiya karkashin inuwar kasa guda da aka sanya mata suna Saudi Arabiya, ko kuma Sa'udiyya.

Gano man fetur da aka yi a shekarun 1930 sun cilla wannan kasa mai ra'ayin 'yan mazan jiya, kuma ta Musulmi, ta shigo cikin karni na 20. Kudaden da ake samu daga man fetur ya janyo gine-gine an zamani da suka mayar da kasar ta zamo mai karfin tattalin arziki.

Thomas Lippman, marubuci kuma malami a Cibiyar Nazarin harkokin Gabas ta Tsakiya a nan Washington, ya ce daya daga cikin muhimman nasarorin da Sarki Fahd ya samu shi ne na tabbatar da jagorancin kasar ta tsallake mawuyacin lokaci mai hatsarin gaske a tarihinta. Ya ce, "Sarki fahd ya tabbatar ad ci gaba da dorewar al'amura a yankin gabas ta tsakiya ta yadda kasar Sa'udiyya ta ci gaba da samun kwanciyar hankali. sai dai kuma abinda yayi takaicinsa daga baya cewar ala tilas ya fita daga kasar ya gayyato Amurka domin ta taimaka wajen kare kasar a bayan da Iraqi ta kai harin mamaye Kuwaiti a 1990."

Gayyato mutanen da ba Musulmi ba zuwa cikin kasar da aka haifi addinin Islama ya harzuka masu kishin Islama, cikinsu har ad shugaban kungiyar al-Qa'ida haifaffen Sa'udiyya, Osama bin Laden. Bin laden yayi misali da kasancewar sojojin Amurka a Sa'udiyya a zaman daya daga cikin dalilansa a lokacin da ya kai hare-hare a Amurka a 2001, da kuma hare-haren da ya kai cikin Sa'udiyya daga baya.

Tun daga lokacin Sa'udiyya take daukar matakan murkushe masu tsagerancin addini, kuma babar kawa ce ta Amurka a yaki da ta'addanci.

Tsohon jakadan Amurka a Hadaddiyar Daular Larabawa, David Mack, yayi hasashen cewa mulki zai koma hannun sabon sarki Abdullahi ba tare da wata tangarda ba. Ya ce, "akwai mutane da dama da suka yi imanin cewa a bayan mutuwar sarki Fahd, Yarima Abdullahi zai dauki kwararan matakai na babu sani babu sabo wajen aiwatar da sauye-sauyen cikin gida, wadanda suka hada da karfafa matsayin mata, da kafa wani tsarin siyasa ko da ane iri ne kuwa, da sauye-sauyen shari'a da na tattalin arziki da kuma sauya tsarin ilmi na kasar.

Jakada Mack ya ce baban abinda ya fi fice a mulkin marigayi Sarki Fahd, shine irin dangantakar kut da kut da ya kulla da Amurka da kuma kasashen yammacin duniya. Ya ce Fahd sarki ne da yayi kokarin mayar da kasarsa ta zamo ta zamani.

XS
SM
MD
LG