Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tarzoma Ta Barke a Titunan Birnin Khartoum


John Garang
Dubban mutane sun fantsama a kan titunan Khartoum, babban birnin Sudan, domin nuna fusata game da mutuwar John Garang, wanda yayi shekaru fiye da ashirin yana jagorancin 'yan tawayen kungiyar SPLA a kudancin kasar. An rantsar da Mr. Garang a zaman mataimakin shugaban kasar Sudan makonni uku kacal da suka shige.

Wakilin Muryar Amurka a yankin gabashin Afirka ya ce halin da ake ciki a birnin Khartoum yana kara yin muni a yayin ad dubban masu zanga-zanga suka fara kona motoci, da farfasa tagogin kantuna.

Kanar Bjarne Giske, shugaban Hukumar Sa Idanu ta Hadin Guiwa dake kula da aiki da shirin tsagaita wuta a yankin tsakiyar Sudan, ya ce 'yan zanga-zangar sun fara gwabzawa ad bindigogi da 'yan sandan Sudan a baban birnin. Amurka tana goyon bayan wanan hukuma.

Kanar Giske ya ce, " an kara yawan 'yan sandan dake kokarin kwantar da wutar wannan sha'ani, kuma sun fara shawo kan zanga-zangar, sai dai kuma ana lalata dukiya sosai, musamman ababen hawa."

An bayar da rahoton cewa tarzoma ta bazu zuwa wasu yankunan kasar, ciki har da Juba, daya daga cikin manyan biranen dake yankin kudancin Sudan. Gidan telebijin na Nation na Kenya ya ce sojojin kungiyar 'yan tawaye at SPLA sun fara gida-gida a birnin na Juba su na kwasar ganima da lalata dukiya. Har ila yau an ce sun bukaci da a kori dubban sojojin gwamnati dake Juba ba tare da jinkiri ba.

Labarin mutuwar John Garang da kuma tarzomar da ta barke a bayan haka, sun girgiza wannan yanki na Afirka, suka kuma dakushe fatar cimma zaman lafiya a wannan kasa dake neman tsamo kai daga yakin basasar shekaru fiye da ashirn.

Mukaddashin shugaban kungiyar SPLA, Salva Kiir Mayardit, yayi hamzarin tabbatarwa da mutane a birnin Khartoum cewa mutuwar Mr. Garang ba zata gurgunta yarjejeniyar zaman lafiyar da ya kulla da shugaba Hassan Omar al-Bashir ba.

Mataimakin na Mr. Garang ya ce, "Kudancin Sudan da kasar Sudan baki daya sun yi rashin da babba. Mataimakin shugaban kasa, kuam shugaban kudancin Sudan ya kai ziyarar aiki zuwa Uganda daga 29 zuwa 30 ga watan nan na Yuli. A lokacin ad yake komowa ranar asabar a kudu da garin Sabon kush sai jirgin saman helkwafta da yake tafiya a ciki ya fadi. Ina tabbatarwa da mutane cewa mus hugabannin SPLA zamu ci gaba da aiwatar da manufofin ad Mr. Garang ya shimfida."

An fara baza labarin mutuwar Mr. garang ranar asabar da maraice. A ranar ta asabar ad rana, ya baro wani filin jirgin saman Uganda a cikin helkwafta a kan hanyarsa ta komawa kudancin Sudan. A ranar lahadi, jami'an Uganda sun tabbatar da cewa jirgin ad yake ciki ya bace. Litinin kuma sai jami'an Majalisar Dinkin Duniya suka tabbatar da cewa Mr. Garang, mai shekaru sittin da haihuwa, ya mutu a hatsarin jirgin.

Jami'an Uganda da na Sudan sun ce jirgin yayi kokarin kaucewa wani yanki mai rashin kyawun yanayi a kan hanyarsa ta komawa gida kafin ya fadi.

XS
SM
MD
LG