Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Tawagar Kungiyar Tarayyar Kasashen Afirka Da Ta Ziyarci Mauritaniya Ya Ce An Tabbatar Musu Da Bukatar Yin Sauyi A Kasar


Shugaban wata tawagar Kungiyar Tarayyar Kasashen Afirka da ta gana da shugaban sabuwar gwamnatin mulkin sojan kasar Mauritaniya, ya ce an tabbatarwa da 'yan tawagar tasa bukatar dajke akwai ta yin sauyi a kasar.

Amma kuma ministan harkokin wajen Nijeriya, Oluyemi Adeniji, ya fada a yau laraba cewar tawagar ta roki Kanar Ely Ould Mohammed Vall da ya gaggauta kaddamar da shirinsa na shimfida mulkin dimokuradiyya da yayi alkawari.

Mr. Adeniji ya ce za a ci gaba da dakatar da Mauritaniya daga cikin Kungiyar Tarayyar Kasashen Afirka har sai an gudanar da zabubbuka na dimokuradiyya.

Sojoji sun yi alkawarin gudanar da zabe cikin shekaru biyu.

Wannan tawaga ta Kungiyar Tarayyar Kasashen Afirkata yi tattaki zuwa Mauritaniya domin ta bukaci sojoji su maido da gwamnatin fararen hula a bayan da suka hambarar da shugaba Maaouiya Ould Sid Ahmed Taya lokacin da yake kasar waje.

Shugaba Ould Taya, wanda ya tafi Jamhuriyar Nijar bayan juyin mulkin, yanzu yana kasar Gambiya, kuma ya shaidawa Muryar Amurka cewa har yanzu shi ne shugaban kasar Mauritaniya.

XS
SM
MD
LG