Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kafa Dokar-ta-baci Yau Asabar A Kasar Sri Lanka


Sri Lanka ta kafa dokar-ta-baci yau asabar, a bayan da aka kashe ministan harkokin waje, kuma babban mashawarcin shugabar kasar.

Sojoji sun kakkafa shingaye suka tare hanyoyi a Colombo, babban birnin kasar, suka kuma fara farautar mutanen da suka kashe ministan. An tsare mutane akalla biyu, amma kuma babu wani karin bayani da aka samu a game da su.

Jami'an soja a birnin na Colombo sun ce ana kyautata zaton 'yan tawayen Tamil Tigers ne suka kashe ministan harkokin waje Lakshman Kadirgamar, ta hanyar buya da harbe shi da bindiga daga nesa. Ita dai shugaba Chandrika Kumaratunga, wadda ta yi rokon da a kwantar da hankula a kuma kai zuciya nesa, ba ta fito fili ta zargi 'yan tawayen da kai wannan harin ba.

Su kansu 'yan tawayen sun ce babu ruwansu da kisan ministan harkokin wajen. Suka ce wannan kisan aikin wani bangare ne a cikin rundunar sojojin kasar wanda yake da wata boyayyiyar manufa ta gurgunta shirin tsagaita wutar da aka shafe fiye da shekatru uku ana aiki da shi.

Ministan harkokin waje Kadirgamar, dan kabilar Tamil ne wanda aka sha yin barazanar kashwa a can baya. An harbe shi a kai da kuma kirji daga can nesa, a jiya jumma'ada maraice a lokacin da yake shakatawa a cikin lambun gidansa, inda tun farko aka dauki matakan tsaro masu yawan gaske. Ya cika yau asabar kafin ketowar alfijir a wani asibiti.

Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Condoleeza Rice, ta yi tur da kisan a a zaman wani mummunan danyen aiki na tayar da hankali, ta kuma roki al'ummar kasar sri Lanka da kada su bari wannan kisa maras kan gado da aka yi wa ministan harkokin wajen mai shekaru 73 da haihuwa ya haddasa tashin hankali a kasar ko kuma ya wargaza shirin tsagaita wuta na 2002.

Shi ma babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Kofi Annan, ya bayyana jijjiga da kuma bakin cikinsa. Jami'an jakadancin kasar Norway, wadanda suka shiga tsakani aka samu tsagaita wuta a yakin basasar da aka jima ana yi a Sri Lanka sun ce mutuwar ministan harkokin wajen koma baya ce babba ga shirin wanzar da zaman lafiya a wannan tsibiri.

XS
SM
MD
LG