Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Kotu A Jamus Ta Samu Dan Kasar Morocco Da Laifin Taimakawa Maharan 11 Ga Watan Satumba A Amurka


Wata kotu a kasar Jamus ta samu wani dan kasar Morocco da laifin da aka tuhume shi na taimakawa 'yan fashin jiragen sama da suka aiwatar da hare-haren ta'addanci na ranar 11 ga watan Satumbar 2001 a kan Amurka.

A bayan da aka sake yi masa shari'a ta tsawon shekara guda, kotun dake birnin Hamburg ta samu Mounir el-Motassadeq da laifin zamowa memba na wata kungiyar ta'addanci, ta kuma yanke masa hukumcin daurin shekaru 7 a kurkuku yau jumma'ar nan.

Sai dai kuma kotun ba ta same shi da babban laifin da aka tuhume shi da aikatawa na sanya hannu a hare-haren kai tsaye ba.

Masu gabatar da kararraki sun bukaci da a yanke masa hukumcin daurin shekaru 15 a kurkuku. Lauyoyin Motassadeq suka ce yana taimakawa 'yan'uwansa Musulmi ne kawai a lokacin da ya aike da kudi ga 'yan fashin jiragen saman, kuma bai san cewa su na shirin kai hare-haren kunar-bakin wake da jirage a kan biranen New York da Washington ba ne.

A shekarar 2003, wata kotu a Hamburg ta samu Motassadeq da laifin taimakawa wajen kai hare-haren, amma kuma kotun daukaka kara ta yi watsi da wannan hukumci a saboda an ki ba da masu kare shi damar ganin shaidar da wasu da ake zaton 'yan al-Qa'ida ne da Amurka ta kama take rike ad su, suka bayar game da shi Motassadeq. Daga baya, hukumomin Amurka sun mikawa kotun takaitaccen bayanin shaidar da mutanen da ake yi wa tambayoyin suka bayar.

XS
SM
MD
LG