Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Hafsan Hafsoshin Sojan Ivory Coast Yayi Barazanar Kawar Da Shugaba Gbagbo Daga Kan Karagar Mulki


Tsohon hafsan hafoshin sojan kasar Ivory Coast, yayi barazanar kawar da shugaba Laurent Gbagbo daga kan karagar mulki.

Janar Mathias Doue ya shaidawa gidan Rediyon Faransa (Radio France International) cewar idan har kasashen duniya sun tashi sun kawar da shugaban cikin lumana ba, to shi zai dauki kowane irin mataki na kawar da Mr. Gbagbo daga kan mulki.

Ya ce kawar da shugaba Laurent Gbagbo daga kan mulki ne kawai zai iya kawo karshen fitinar shekaru uku a tsakanin 'yan tawaye da gwamnati.

Janar Doue shi ne jagoran rundunar sojojin kasar Ivory Coast kafin shugaba Gbagbo ya maye gurbinsa a watan Nuwamba. Ana daukarsa a zaman mai sassaucin ra'ayin siyasa.

A halin da ake ciki, tsohon kakakin sojojin kasar ta Ivory Coast, Jules Yao Yao, ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa a yau asabar cewa da yawa daga cikin sojojin kasar sun shirya kalubalantar shugaba Gbagbo.

An raba kasar Ivory Coast gida biyu tun lokacin da yakin basasa ya barke a 2002. Har yanzu babu wani ci gaban kirki da aka samu wajen aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiyar da aka kulla a tsakanin gwamnati da 'yan tawaye.

XS
SM
MD
LG