Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin Man Shell Ya Sake Bude Wasu Rijiyoyinsa Biyu A Kudancin Nijeriya


Kamfanin mai na Shell ya ce ya koma ga aikin sarrafa danyen mai a wasu tasoshinsa biyu da aka rufe saboda zanga-zangar mutanen yankin da rijiyoyin suke a kudancin Nijeriya.

Kamfanin man na Shell ya ce a jiya lahadi ya bude tashar tura man Agbada 1, mai samar da ganga dubu 14 na danyen man fetur a kowace rana. A yau litinin kuma, ’yan zanga zanga sun tattara nasu ya nasu suka bar tasha ta biyu, wadda aka sake budewa ta ci gaba da aikin samar da ganga dubu 25 a kowace rana.

A makon jiya ’yan zanga-zanga suka kewaye masana’antar a yankin Niger Delta su na neman da a kara yawan kudin diyyar da aka ware musu a bayan yoyon mai shekaru biyun da suka shige, wanda suka ce ya lalata musu gonaki da kuma wuraren kamun kifi. Mutanen kauyen sun nemi da sai lallai a biya su dala miliyan dubu biyar na Amurka, suka ki yarda da dala dubu 900 na Amurka da kamfanin Shell ya ba su.

Kamfanin dillancin labarai na AP ya ce za a ci gaba da tattaunawa tsakanin bangarorin biyu a kan wannan batu.

XS
SM
MD
LG