Wani shugaban kungiyar kishin Falasdinu ta Hamas da ake nema ruwa a jallo ya fito a cikin wani faifan bidiyo yana bayyana janyewar da Isra’ila ta yi daga zirin Gaza a zaman nasara ga ’yan kishin Falasdinu.
A yau asabar kafofin labarai na kasashen yammaci dake Gaza suka samu kofen wannan faifan bidiyo.
A cikinsa, wani mutumin da aka boye kamanninsa baki daya (dubi hoton sama) ya bayyana cewa shine dan hada bama-bamai da ake nema ruwa a jallo, Mohammed Deif. Yayi kira ga Falasdinawa da su ci gaba da gwagwarmaya da bani Isra’ila har sai an murkushe kasar ta yahudawa.
Har ila yau ya ja kunnen majalisar mulkin kan Falasdinawa da kada ta nemi kwace makaman kungiyoyin ’yan gwagwarmaya.
Jami’an Isra’ila sun ce faifan bidiyon ya nuna bukatar dake akwai ga majalisar mulkin kan Falasdinawa ta dauki matakan murkushe ’yan gwagwarmaya. Jami’an Falasdinawa sun ce duk da wannan furuci, har yanzu kungiyar Hamas tana da kudurin ci gaba da yin aiki da yarjejeniyar tsagaita wutar da aka yi watanni 6 ana aiki da ita.