Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Mayakan Saman Amurka Zata Kyale Sojoji 300 Su Komo Gida Daga Iraqi Da Afghanistan


Rundunar mayakan saman Amurka ta ce zata maido da sojojin sama su 300 zuwa gida daga Iraqi da Afghanistan, domin su taimakawa iyalansu wajen kokarin farfadowa daga mahaukaciyar guguwa ta Katrina.

Wani kakakin rundunar mayakan samar ya fada a yau asabar cewa a cikin makonni biyun da suke tafe wadannan sojojin na sama, dukkansu daga sansanin mayakan saman Keesler dake garin Biloxi a Jihar Mississippi, zasu fara tasowa zuwa gida.

Sojojin sun hada da wadanda tun farko aka shirya zasu komo gida cikin watan nan na Satumba da kuma wadanda aka rage musu tsawon lokacin aiki domin su komo.

Mahaukaciyar guguwar ta Katrina ta yi mummunar barna a wannan sansanin mayakan sama na Keesler, inda ta tafi da mafi yawan gidajen dake cikin sansanin da kuma kayayyakin bukatun dake can, kamar hanyoyi da wayoyin lantarki da na tarho da makamantansu.

XS
SM
MD
LG