Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Olusegun Obasanjo Ya Bayar Da Umurnin A Binciki Zargin Da Ake Yi Masa


Shugaba Olusegun Obasanjo na Nijeriya ya bayar da umurnin da a gudanar da binciken zargin da aka yi masa na zarmiya da cin hanci.

Shugaba Obasanjo ya bayar da wannan umurni jiya jumma’a a bayan wannan zargi da gwamna Orji Uzo Kalu na Jihar Abia yayi masa.

Mr. Kalu ya zargi shugaba Obasanjo da laifin sace kudi daga baitulmalin gwamnati, da rike asusun kudi a wani bankin kasar waje, abinda doka ta haramtawa mai rike da mukamin gwamnati a Nijeriya, tare da karbar makudan kudade daga hannun ’yan kwangilar mai da na tsaro.

Shugaba Obasanjo ya musanta wannan zargi.

Hukumar Bin Kadin Laifuffukan tattalin arziki da na zamba ta Nuhu Ribadu ita ce zata gudanar da binciken wannan lamarin.

Mr. Kalu yana daya daga cikin masu sukar lamirin shugaba Obasanjo koda yake dukkansu ’yan jam’iyyar PDP mai mulkin kasar ce. Mr. Kalu ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2007.

XS
SM
MD
LG