Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yansandan kasar Indonesia suna rike da mutane biyu dangane da Harin ranar Asabar


‘Yansanda kasar Indonesia sunce ayanzu haka suna yiwa wasu mutane biyu tambayoyi game da harin bam ba kunar bakin wakin nan na ranar Asabar wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane ashirin da biyu. Babban ‘yansandan birnin Bali, ya fada ayau Talata cewa akwai kwararan dalilai da suka danganta wadannan mutane biyu da suka kama da hannu a wannan harin Bam, duk da haka tambayoyi kawai ake musu. ‘Yansandan sunyin amfani ne da hotunan Video na ‘yan yawon shakatawa da kuma gangar kawunan wadanda ake jin sune ‘yan kunan bakin waken, wajen nunawa mutane ko zasu shaida wasu daga cikinsu. Jami’an kasar ta Indonesia sunce suna jin kungiyar ‘yan yakin sakai na Jamaah Islamiya ce ta kai wannan harin. Kasar Australia ta gargadi ‘yan kasarta da suyi taka tsantsan da wannan yanki na kasar Indonesiya. Ma’aikatar harkokin wajen kasar tace tun daga ranar waccan Asabar ne ‘yan ta’adda su kayi barazana cewa zasu kara kai wasu hare haren a club-club na garin Seminyak, inda aka fi samun baki ‘yan yawon bude ido daga kasashen yammaci.

XS
SM
MD
LG