Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amirkawa biyu da ba-faranshe, sun sami lambar yabo ta Nobel


Amirkawa biyu da dan kasar Faransa daya sun sami kyautar lambar yabo ta Nobel a fannin binciken kimiyyar hada magunguna ta (Chemistry). Yau Laraba ne aka baiwa, Robert Grubbs da Richard R. Schrock Amirkawa biyu, da Yves Chauvin ba-Faranshe wannan lambar yabo a cibiyar binciken da nazarin ilmin kimiyya na kasar Sweden da birnin Stockholm. Wadannan masana ilmin kimiyya ukun an basu lambar yabon ne domin fice da sukayi a kokarin samo magunguna da kuma robobi na anfanin jama'a da basu da illa ga muhalli. Masanan uku zasu raba dala miliyon daya da dubu dari uku da za'a basu a wajen wani kasaitaccen buki da za'ay a ranar goma ga watan Disamba mai zuwa.XS
SM
MD
LG