Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ma'aikatar shari'ar Amirka zata binciki dukan bakar fata,  Robert Davis...


Ma’aikatar shari’a ta Amirka ta fara wani bincike don kare hakkin wani bakar fata dan shekaru 64 da haifuwa da ‘yansanda suka masa duka a birnin New Orleans inda guguwar Katrina ta daidaita. Wannan bincike da aka bada sanawarsa jiya Litinin ya biyo bayan wani Hoton Bidiyo da aka nuna a gidajen Talbijin, da ya nuna wasu ‘yansanda biyu cikin kaki a birnin New Orleans suna dukan wani mutun mai suna Robert Davis a fuska da kuma sauran jikinsa lokacin da suka kamashi bisa zargin ya sha barasa ya fito bainar jama’a yana tangaririya. Hoton Bidiyon yanuna wani dan sanda kuma, ya kama wuyan wani ma’aikacin talbijin wanda ya dauki hoton lokacin da suke dukan Robert Davis. Shi dai Mr. Davis yace baisha giya ba. A lokacin da suka tareshi, yace ya fito ne neman taba sigari. Ya fadawa gidan Talbijin na CNN cewa wannan al’amari ya farune lokacin da yake Magana da wani dansanda dake kan doki, sai wani dan sanda ya sa musu baki, sai yace wa dansandan wannan ba daidai bane, shikenan dan sandan ya harzuka. Lauyan Mr. Davis, Joseph Bruno yace Mr. Davis baya jin cewa ‘yansandan sun masa wannan dukar ne don shi baker fata. ‘Yansandan uku farar fata ne, an gansu a bidiyo a gaban kotu, suna cewa basu aikata laifi ba. Tunin dai an dakatar dasu daga aiki, sai yadda hali yayi.

XS
SM
MD
LG