Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gidaje Fiye Da Miliyan Uku Suka Rasa Wutar Lantarki A Sanadin Wilma


Hukumar kula da yanayi ta nan Amurka ta ce mahaukaciyar guguwar nan mai suna "Wilma" tana tattare da iska mai kadawar kilomita 200 cikin sa’a daya, kuma tana ratsawa ta kan teku daura da gabar gabashin wannan kasa.

Wilma ta keta ta kan Jihar Florida a kudancin wannan kasa yau litinin, ta kashe mutane akalla hudu. Jami’ai suka ce Wilma ta haddasa ambaliya mai tsanani, ta tuge bishiyoyi da sandunan wayoyin lantarki, ta maida su tamkar makamai.

Suka ce gidaje fiye da miliyan uku ne ba su da wutar lantarki a yanzu haka.

Shugaba Bush ya ayyana kananan hukumomi da dama a Jihar ta Florida a zaman yankunan da bala’i ya abkawa. Jami’an Hukumar agajin gaggawa ta tarayya, wadda aka soki lamirin jan kafar da ta yi wajen tallafawa wadanda mahaukaciyar guguwa ta Katrina ta shafa, sun ce suna aiki kafada da kafada da hukumomin jiha da na kananan hukumomi domin agazawa mutanen da Wilma ta shafa.

A halin da ake ciki, masana yanayi sun ce gagarumin hadarin ruwan sama mai suna "Alpha" shi ma yana ratsawa daura da gabar gabashin Amurka, kuma nan da sa’o’i 12 zai hade da mahaukaciyar guguwa ta wilma. Ana sa ran idan suka hadu zasu haddasa ruwan sama mai tsanani da kuma ambaliyar ruwa yau talata a nan yankin gabashin Amurka.

XS
SM
MD
LG