Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Adawa A Tsibirin Zanzibar Sun Ce Sune Ke Kan Gaba A Sakamakon Farko Na Zaben Da Aka Gudanar


'Yan adawa a tsibirin Zanzibar mai cin gashin kai a kasar Tanzaniya sun ce suke kan gaba a sakamakon farko na zaben da ya zamo fitina a wasu wurare, wasu kuma aka yi ta zargin magudi.

Dan takarar shugaban kasa na adawa, Seif Sharif Hamad, ya ce sakamakon da aka samu ya zuwa yanzu daga rumfunan zabe, ya nuna cewa jam'iyyarsa ta "Civic United Front" tana kan gaba da kashi 60 daga cikin 100 na kuri'u.

Babu wani sakamakon da hukuma ta bayar ad hannunta, kuma ba a ji furucin komai ba daga bakin jam'iyyar "Chama Cha Mapinduzi" mai mulkin kasar.

A lokacin jefa kuri'a jiya lahadi, 'yan sanda sun harba barkonon tsohuwa da kuma ruwan zafi a kan magoya bayan jam'iyyun adawa.

An samu tashin hankula a rumfunan zabe da dama, kuma ya biyo bayan yunkurin da sojoji suka yi na kawo wasu mutane cike da motocin safa wadanda 'yan adawa suka ce mutane ne da ba su yi rajista daga yankunan karkara.

Ana gwagwagwa sosai a wannan zabe an shugaban kasa ad 'yan majalisar dokoki a tsakanin 'yan gurguzu wadanda suka yi shekaru fiye da talatin suna mulkin wannan tsibiri mai kwarya-kwaryar ikon cin gashin kai da kuma 'yan adawa da suka yi alkawarin gudanar ad muhimman sauye-sauye.

XS
SM
MD
LG