Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Samu Karin Tashin Hankali A Iraqi A Yayin Da Shugabanni Ke Tattaunawar Neman Sasantawa


A Iraqi, wani dan harin kunar-bakin-wake a cikin mota ya kai hari a kan Musulmi 'yan mazhabin Shi'a dake zaman karbar gaisuwar mutuwa asabar din nan, ya kashe mutane akalla 30, ya raunata wasu 40.

'Yan sanda a garin Abu Saida dake kusa da Baquba, sun ce wannan dan harin bam ya tuka motarsa cikin wani tanti inda aka taru ana karbar gaisuwar mutuwa, ya tayar da bama-baman dake cikin motar.

Tun da fari a wata unguwa dake kudu maso gabashin Bagadaza an kashe mutane akalla 13, wasu 20 suka ji rauni a lokacin da bam ya tashi cikin wata mota a kasuwar dake cike da mutane.

A birnin Mosul, 'yan sandan Iraqi da sojojin Amurka sun gwabza da 'yan tawaye, suka kashe 'yan ta-kife 8.

Har ila yau, 'yan sandan Iraqi sun ce an kama mutane hudu dangane da hare-haren bam da aka kai kan wasu masallatai biyu ranar jumma'a, har aka kashe mutane kusan 80 a garin Khanaqin wanda yawancin al'ummarsa Kurdawa ne.

Yayin da wannan tashin hankali ke ci gaba da wakana, shugabannin dake wakiltar al'ummar Shi'a da Kurdawa da kuma larabawa 'yan sunni da aka kabe hannayensu daga sha'anin mulki, sun fara wani taron sasantawa na tsawon kwanaki uku a birnin al-Qahira. Makasudin wannan tattaunawa da Kungiyar Kasashen Larabawa ta shirya shine hana rikici a tsakanin mazhabobin Iraqi mamaye kasar.

XS
SM
MD
LG