Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Kenya ya nada sabbin ministoci


Shugaba Mwai Kibaki na Kenya ya nada sabuwar majalisar ministocinsa da yayi wa garambawul inda ya rike wadanda suka goyi bayan chanje-chanjen da yaso wa kundin tsarin mulki, ya zubar da wadanda basu ba shi goyon bayan ba. A cikin jawabin da ya wa kasar baki daya ta gidan Talbijin inda ya bayyana sunayen ministocin nasa a yau Laraba, shugaba Kibaki yace ya bar wasu daga cikin ministocin akan tsofaffin mukamansu, kamar ministan tsaro John Michuki, na kuddi David Mwiraria da kuma ta lafiya Charity Ngilu. Amma tsohon ministan watsa labarai Rafael Tuju yanzu an maida shi ministan harakokin waje yayinda ma’aikatar watsa labaran kuma aka bada ta ga Muthi Kagwe. Tun bayanda ya sha kasa a yunkurin da yayi na chanja kundin tsarin mulkin a ran 21 ga watan Nuwamban da ya gabata ne, shugaba Kibaki ya wargaza gwamnatin tasa. Masu sukar lamirin chanjin da shugaban yaso yayi sunce yaso ya karawa kansa iko ne, ya rage ikon frayim-minista. Wannan yunkurin yiwa kundin tsarin mulki kwaskwarima ya janyo rabuwar kawunan kusoshin gwamnatin ta Kibaki, ya kuma haddasa tarukkan gangami masu yawa da aka yi ta tashe-tashen hankulla a lokacin yinsu.
XS
SM
MD
LG