Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gobara ta lafa a Kamfanin Shell a Nigeria


Kamfanin Mai na Shell a Nigeria yace an kashe wutar dake ci tun ranar Talata a wasu hanyoyin aikewa da mai zuwa tasoshinsa na Mai. Mai Magana da yawun kamfanin Mai na Shell yace ma’aikatan kamfanin sun fara gyara sandunan aikewa da Man wadanda suka kone, kwanaki uku kenan bayan da wasu suka sa wutar wacce ta yi sanadiyyar mutuwar mutane akallan 8. Kamfanin Mai na Shell, Mallakar kasar Poland, yace har yanzu adadin mai da ake samarwa a Nigeria a rana ya ragu da kima ganga 180 a kowace rana saboda wannan gobarar. Jiya Alhamis, shugaban Nigeria Chief Olusegun Obasanjo, ya tura jama’ian tsaro zuwa yankundan kasar masu albarkatun man Fetur domin zaman cikin shirin ko ta kwana. Shugaban ya lashi takwabi akan zai hukunta duk wanda aka kama da hannu a tashin gobarar ranar Talatan. Jami’ai a yankin kudancin kasar sunce matasane wadanda ke cike da fushi suka tada gobarar. Su kuwa mazauna yankun dake da albarkatun man fetur a kasar sunsha kukar cewa gwamnati na samun biliyoyin dala ayankunansu, amma bata kula da su ba.

XS
SM
MD
LG