Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Litinin Din Nan Ake Tuna Cikar Shekara Guda da Mummunar Igiyar Ruwa Ta Tsunami Wadda Ta Kashe Dubbai A Yankunan Bakin Gabar Tekun Indiya


Gobe litinin ake tuna cikar shekara guda da mahaukaciyar igiyar ruwa ta "Tsunami" wadda ta ragargaza bakin gabar tekun Indiya, kama daga kasar malaysia a gabas har zuwa bakin gabar Afirka a yamma, kuma tuni har an fara gudanar da tarurruka na tunawa da wadanda suka rasa rayukansu.

Jiya asabar a Thailand, wasu masu jimami sun yi addu'o'i, wasu suka yi shiru na wani lokaci, yayin da wata 'yan wata kabilar masunta dake yawo cikin teku a kasar, Moker, suka yi ta buga ganguna suna gudanar da irin nasu addu'o'in na gargajiya.

Mahaukaciyar igiyar ruwa ta "Tsunami" wadda girgizar kasar da aka yi a karkashin teku a dab da gabar tsibirin Sumatra ta haddasa, ta kashe mutane fiye da dubu 200, yayin da wasu fiye da miliyan biyu suka rasa gidajensu.

An shirya bukukuwa da dama gobe litinin, a lokacin da mutanen da suka kubuta da rayukansu, da 'yan'uwan mutanen ad suka mutu da jami'an gwamnati da wasu a yankin da kuma a fadin duniya zasu tuna da wannan rana ta daya daga cikin bala'o'i mafi muni da bil Adama ya taba gani.

XS
SM
MD
LG