Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane A Fadin Duniya Suna Jimamin Mutuwar Shugaban Kosovo, Ibrahim Rugova


Shugaba Ibrahim Rugova na yankin Kosovo ya rasu yana da shekaru 61 da haihuwa, a sanadin cutar sankarar huhu, kwanaki kadan kafin Majalisar Dinkin Duniya, MDD, ta gudanar da tattaunawa a kan makomar wannan lardi na jamhuriyar serbia.

Ibrahim Rugova ya zamo shugaban lardin na Kosovo a shekarar 2002. Ana daukarsa a zaman uba ga gwagwarmayar neman 'yanci na 'yan kabilar Aklbaniyawan yankin.

Jami'an MDD sun ce an dage wannan tattaunawa, wadda aka shirya zata kunshi batun 'yancin lardin daga Serbia, har sai cikin wata mai zuwa na Fabrairu.

Shugabannin kasashen duniya sun yi ta aikewa da sakonninsu na ta'aziyya a duk tsawon rana jiya asabar. Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Condoleeza Ricce, ta ce duniya tana mutunta marigayi Ibrahim Rugova a saboda yadda ya fifita dimokuradiyya da zaman lafiya a yayin da Kosovo ke fuskantar kalubale.

Shugaba Jacques Chirac na Faransa ya yabawa Mr. Rugova a saboda akidarsa ta zamantakewa, da yin sulhu.

Shugaba Boris Tadic na Serbia ya ce wannan mutuwa babbar hasara ce ga Kosovo.

XS
SM
MD
LG