Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An zabi shugaban Kongo ya zama shugaban kungiyar tarayyar Afirka


Shugabannin kasashen Afrika dake taron kungiyar tarayyar Afrika a kasar Sudan sun zabi janhuriyar Congo ta shugabanci kungiyar yayinda su ka cire kasar Sudan saboda matsalarta na rashin kiyaye hakkin Dan Adama. A karkashin wata yarjejeniyar yi da wajewa da aka kulla da kasar Sudan din, a yau Talata, sai shekata ta dubu 2 da 7 zata karbi kujeran shugabancin kungiyar.

Shugaba kasar Burkina Faso Blaise Campaore yace kasashen kungiyar Tarayyar Afrika za su taimakawa kasar Sudan ta gyara halayenta ta kuma warware matsalolin cikin kasarta kafin lokacin da zata karbi ragamar shugabancin kungiyar. Wannan shawarar da kungiyar ta yanke a yau ya saba al’adar kungiyar wacce bisa ka’idarta duk kasar da a kayi taron koli a cikinta, itace zata zama shugabar kungiyar mai kasashe 53. Ita dai kasar Sudan har zuwa ranar Asabar waccan tana matsa hannu na samun wannan mukamin.

To amma kungiyoyin kare hakkin Bil adama sun nuna matukar kiyayyarsu ga baiwa kasar Sudan mukamin saboda tashe-tashen hankula dake wakana a kasar da kuma yadda take kiyaye hakkiin Bil adama a yankin Darfur. A yanzu haka shugaban kasar Congo Sassou Nguesso shine ya zama shugaban wannan kungiya ta tarayyar Afrika.

XS
SM
MD
LG